(ABNA24.com) Shugaban gwamnatin hadin kan kasa ta Libiya, Fayez el-Sararj, ya bukaci a koma kan tattaunwar siyasa karkashin MDD domin shawo kan rikicin kasar.
Kiran na El-Saraj, na zuwa ne a daidai lokacin da ya kaddamar da farmaki kan wani sansanin sojin saman al-Watiya, dake hannun abokin rikicinsa Khalifa Haftar, saidai ba tare da yin nasara ba.
A wata sanarwa da gwamnatin ta Tripoli, ta fitar, ta ce, Fayez el-Sarraj, a shirye yake kan kiran da akayi na samar da mafitar siyasa a rikicin kasar da kuma kawo karshen sabanin dake akwai.
A kusan mako guda da ya gabata ne, shugaban gwamnatin ta Tripoli, ya yi watsi da shelar da Khalifa Haftar dake rike ikon gabashin kasar ya yi, na tsagaita wutar jin kai alfarmar watan Ramadana.
/129
7 Mayu 2020 - 04:31
Lambar labari: 1034340
Shugaban gwamnatin hadin kan kasa ta Libiya, Fayez el-Sararj, ya bukaci a koma kan tattaunwar siyasa karkashin MDD domin shawo kan rikicin kasar.